IQNA

Wata Yarinya Mai Fama Da Cutar Shanyewar Bangaren jiki Kuma Take Hardar Kur'ani mai Tsarki

21:24 - October 03, 2021
Lambar Labari: 3486381
Tehran (IQNA) Neda Ahmad wata yarinya ce da take fama da shanyewar bangaren jiki wadda kuma ta hardace surori da dama na kur'ani.

Shafin yada labarai na sadal balad ya bayar da rahoton cewa, Neda Ahmad daga lardin Qana na kasar masar, yarinya ce da take fama da matsalar cutar shanyewar wani bangaren jiki wadda kuma ta hardace surori da dama na kur'ani a cikin irin wannan yanayi.

Rahoton ya ce, tun daga lokacin haihuwarta, Neda tana fama da matsalar shanyewar wani bangaren jiki, amma kuma duk da haka mahaifanta suna koyar da ita karatun kur'ani, kafin daga bisani mahaifinta ya fara kai ta makarantar kur'ani.

A cikin irin wannan yanayi ta iya koyon karatun kur'ani da kuma hardace surori masu yawa, inda a halin yanzu ta hardace izihi kusan ashirin a kanta.

Neda tana daga cikin yara masu hazaka wadanda babban malamin Azhar Sheikh Ahmad tayyib ya gana da su, kuma ta roke shi da a kafa doka a kasar Masar wadda za ta haramta cutar da masu larura ta musamman a kasar ko kuma yi musu izgili saboda larurarsu.

Mahaifin Neda ya bayyana cewa, duk da cewa diyasa ba ta je makarantar boko ba, amma ta iya magana da harshen turancin Ingilishi, kuma ta iya mu'amala da shafukan yanar gizo da kafofin sada zumunta.

 

4001720

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha