Kamfanin dillancin labaran sputnik na kasar Rasha ya bayar da rahoton cewa, a yau kungiyar ta sanar da ragargaza wani sansanin 'yan ta'adda na Daesh a birnin kabul, tare da kashe wani adadi na 'yan ta'addan.
Mai magana da yawun kungiyar Talin Zabihullah Mujahid ya sanar a shafinsa na twitter cewa, tun a daren jiya ne mayakan Taliban suka fara kaddamar da hare-haren a kan wani sansanin 'yan ta'adda na daesh a kusa da birnin kabul har zuwa safiyar yau Litinin.
Ya ce mayakan nasu sun samu nasarar rusa wannan sansani, tare da kashe dukkanin mayakan Daesh da suke cikin sansanin.
Tun bayan da kungiyar Taliban ta kwace iko da kasar Afghanistan, ta sha alwashin shiga kafar wando daya da 'yan ta'addan Daesh, inda kungiyar ta ce ba su da wurin zama a cikin Afghanistan.
Zabihullah Mujahid bai yi karin bayani kan ko farmakin na Taliban yana a matsayin martani ne ba, kan mummunan harin da 'yan ta'addan daesh suka kaddamar a jiya Lahadi a wani babban masallaci da ke birnin kabul.