IQNA

Taron Murnar Maulidin Manzon Allah (SAW) A Kasar Yemen

16:14 - October 12, 2021
Lambar Labari: 3486415
Tehran (IQNA) al'ummar kasar Yemen sun fara gudanar da tarukan murnar zagayowar lokacin Maulidin manzon Allah (SAW)

Shafin yada labarai na Ansarullah ya bayar da rahoton cewa, al'ummar kasar Yemen sun fara gudanar da tarukan murnar zagayowar lokacin Maulidin manzon Allah (SAW), wanda yake gudana a birane daban-daban na kasar, tare da halartar miliyoyin musulmi.

Baya ga kasar Yemen ma musulmi a kasashen duniya daban-daban sun fara gudanar da tarukar murnar zagayowar lokacin maulidin manzon Allah (SAW).
 
A kasashe da dama na duniya an fara gudanar da tarukan murnar zagayowar lokacin maulidin manzon Allah ne tun daga farkon wanann wata na Rabiul Awwal, wanda shi ne watan haihuwar fiyayyen halitta manzon Allah Muhammad (SAW).
 
An fara gudanar da irin wadanan taruka a kasashe da dama na arewaci da yammacin nahiyar Afirka, da suka hada da Aljeriya, Morocco, Tunisia, Mauritania, Sudan masar, Libya da sauransu, haka nan kasashe irin su Najeriya, Nijar, Mali Senegal Guinea duk an fara gudanar da irin wadannan taruka.
 
A yankin gabas ta tsakiya ma kasashe irin su Iran, Iraki, Oman, Lebanon, Turkiya, Syria, da kuma gabashin Asia, da hakan ya hada kasashe irin su Indonesia, Malaysia tuni suka fara tarukan maulidin manzon Allah.
 

4004226

 

 

 

captcha