IQNA

Nasrullah: Ana Son Yin Amfani Da 'Yan Ta'addan Daesh Ne Wajen Haifar Da Fitina A Cikin Afghanistan

21:00 - October 12, 2021
Lambar Labari: 3486418
Tehran (IQNA) babban sakataren Hizbullah ya bayyana cewa, Amurka tana son ta yi amfani da Daesh wajen haifar da yakin cikin gida a Afghanistan

Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta Lebanon ya yi Allah wadai da munanan hare-haren kungiyar Da’esh ta kai kan masallacin lardin Kunduz da ke arewa maso gabashin Afghanistan.
 
Ya ce,  ta hanyar kaddamar da ire iren wadannan hare haren, kungiyar na da nufin haifar da tashin hankali da jefa Afghanistan cikin yakin basasa.
 
Sayyed Hassan Nasrallah ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin a ranar Litinin, kwanaki kadan bayan wani mummunan harin bam da aka kai kan masu ibada na Afghanistan da ke sallar Juma'a a masallacin da ke yankin Khanabad Bandar a Kunduz ya kashe mutane da dama.
 
Shugaban na Hezbollah ya ce, "Aikin Daesh a yau shi ne haifar da wani yanayin tashin hankali na cikin gida wanda zai haifar da yakin basasa a Afghanistan," ya kara da cewa "alhakin hukumomin Afghanistan na yanzu shi ne kare 'yan kasa ba tare da la'akari da addininsu ko mazhabarsu ba."
 
Mutane sama da hamsin aka rawaito sun rasa rayukansu a harin na ranar Juma’a data gabata kana wasu sama da 100 suka jikkata a harin da kungiyar IS, ta dauki alhakin kai wa.
 

 

4004124

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa:
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha