IQNA

Guterres: Za Mu Ci Gaba Da Kasancewa A Afghanistan Domin Taimaka Ma Matan Kasar

16:33 - October 24, 2021
Lambar Labari: 3486468
Tehran (IQNA) babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa ma'aikatan Majalisar za su ci gaba da ayyukansu a Afganistan har sai 'yan mata sun koma makaranta.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa Majalisar za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta a kasar Afganistan har sai 'yan mata sun koma makaranta, kuma mata ma’aikata su koma bakin aiki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Sputnik cewa, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, Majalisar Dinkin Duniya za ta ci gaba da aiki a Afganistan don kare hakkin mata da 'yan mata.
 
Ya ce: “Za mu jira har sai ‘yan matan sun koma makaranta, sannan mata ma’aikata su koma koma bakin ayyukansu kuma su shiga cikin al’umma,”
 
Sama da wata guda kenan 'yan mata ba sa zuwa makaranta a aji shida, yayin da kuma an bude makarantun samari maza suna zuwa ajujuwansu ba tare da takura ba.
 
Wani mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya shaidawa jaridar The Hill cewa, kimanin jami'an sojin saman Afganistan 150 da suka hada da matuka jiragen sama ne za a dauke su daga Tajikistan zuwa wani wuri na daban, amma bai bayyana takamaiman lokacin ba.
 
Yayin da Amurka ta janye sojojinta daga Afganistan a cikin watan Agusta, ta kuma tura da dama daga cikin sojojin saman Afghanistan da matukan jirgi zuwa Tajikistan da ke makwabtaka da kasar ta Afghanistan.
 
 

4007475

 

Abubuwan Da Ya Shafa: majalisar dinkin duniya ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha