IQNA

Sojojin Gwamnatin San'a A Yemen Na Gab Da Kammala Kwato Lardin Ma'arib Daga Hannun Dakarun Hadi

20:53 - October 27, 2021
Lambar Labari: 3486484
Tehran (IQNA) sojojin gwamnatin San'a a Yemen na gab da kammala kwato lardin Ma'arib daga hannun dakarun Hadi.

Sojojin kasar Yemen da na sa kai sun sami karin nasarori a safiyar yau Laraba a lardin Ma’arib na tsakiyar kasar. Sannan sojojin Saudiya sun fara janyewa daga lardin.

Kafafen yada labarai na kasar Yemen sun bada sanarwan cewa sojojin Yemen da masu sa kai sun sami nasarar kwace iko da yankin Aljuba na kudancin lardin Ma’arib bayan sun sami fahintar juna da mutanen yankin.
 
Har’ila yau sun yi kawanya ga yankin Jabal Murad shi ma daga kudancin kasar ta Yemen.
 
Banda haka wasu majiyoyin sun bayyana cewa sojojin Hadi da na kawancen Saudiya sun fara janyewa daga kudancin lardin Ma’arib a safiyar yau Laraba.
 
Lardin Ma’arib dai ya na da arzikin man fetur da gas don haka ne ya ke da muhimmanci a fagen tattalin arziki a kasar. Masana sun bayyana cewa idan Saudiya da kawayenta sun rasa lardin ma’arin an sami nasara a kansu ke nan a mamayar da sukewa kasar ta Yemen tun shekara ta ta dubu biyu da goma sha biyar.
 

4008363

 

Abubuwan Da Ya Shafa: lardin Maarib
captcha