IQNA

An Gudanar Da Taron Kasashe Makwabtan Kasar Afghanistan A Kasar Iran

20:37 - October 28, 2021
Lambar Labari: 3486486
Tehran (IQNA) Abdollahian, ya bayyana halin da kasar Afghanistan ta tsunduma da cewa hakan sakamako ne shishigin kasashen waje.
Ministan harkokin wajen kasar Iran, Hossein Amir Abdollahian, ya bayyana halin da kasar Afghanistan ta tsunduma da cewa hakan sakamako ne shishigin kasashen ketare.
 
Ya danganta hakan da shiga yakin da Amurka ta yi a kasar ta Afghanistan yau da shekaru ashirin da suka gabata bisa fakewa da yaki da ta’addanci.
 
Mista Abdollahian, ya bayyana hakan ne yayin taron kasashe shida makwabtan Afghanistan gami da Rasha, wanda Iran ta karbi bakuncinsa a jiya Laraba.
 
Ya bayyana cewa, kasashe makobtan na Afghanistan, idan suka karfafa junansu zasu iya taka mahimmiyar rawa wajen hada kan bangarorin siyasa da kabilu na Afghanistan da kuma taimakwa wajen magnace rikicin kasar.
 
A jiya ne aka bude taron ministocin harkokin waje na kasashe shida makobtan Afghanistan a Tehran
 
Manufar taron shi ne hada kai don taimakawa wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin kudancin Asiya.
 
Mahalarta taron sun hada da ministocin harkokin wajen Iran, Pakistan, Turkmenistan, Tajikistan da Uzbekistan, da jakadun Rasha da China.
 
Sai kuma ministocin harkokin wajen Rasha da kuma babban sakataren MDD da suka halarci taron ta kafar bidiyo.
 
Bangarorin sun jadada bukatar hada kai domin isar da kayan agaji da tallafi wa kasar ta Afghanistan, da kuma wajabcin damawa da dukkan bangarori domin samar da zaman lafiya.
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4008456
captcha