
Shafin yada labarai ya bayar da rahoton cewa, ministan harkokin addini na kasar Masar Muhammad Mukhtar Juma'a ya bayyana cewa, ana shirin fara bude ajujuwan hardar kur'ani an cikin masalatai a kasar.
Ministan na Masar ya jaddada cewa, ana shirye-shiryen gudanar da wadannan darussa da kuma gayyato amintattun malamai haddar kur'ani.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin da aka gudanar a Kwalejin Ilimi ta kasa da kasa, Mukhtar Juma ya ce: “A cikin masallatai za a ware wuraren koyar da yara harda Alkur’ani.
Ministan na Masar ya kara da cewa ana iya gudanar da wasu darussan hardar Alkur'ani a masallatai da cibiyoyin matasa ko makarantu.
4009317