IQNA

Dakarun Iran Sun Nuna Hoton Bidiyo Na Yadda Suka Kwato Jirgin Man Iran Da Amurka Ta yi Fashinsa A Cikin Teku

16:58 - November 04, 2021
Lambar Labari: 3486512
Tehran (IQNA) Dakarun Iran sun fitar da cikakken faifan bidiyon arangamar da suka yi da Amurkawa 'yan fashin teku.

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun fitar da cikakken faifan bidiyon arangamar da suka yi a karshen watan da ya gabata, kan wani matakin da Amurka ta dauka na yin fashin teku a kan wani jirgin ruwan Iran.

Lamarin dai ya faru ne a ranar 25 ga watan Oktoba, amma an fitar da labarai da hotunan abin da ya faru a ranar jiya Laraba.

Sojojin Amurka sun kwace jirgin ruwan dakon man fetur na kasar Iran a tekun Oman mai matukar muhimmanci, inda suka mika danyen man da yake dauke da shi zuwa wani jirgin ruwa.

Daga nan ne dai rundunar ta IRGC ta kai farmaki kan jirgin ruwa na biyu, inda ta saukar da jiragenta masu saukar ungulu a kan rufinsa, tare da tilasta jirgin ya karkata akalarsa zuwa gabar ruwa ta Iran.

 

4010451

 

 

captcha