IQNA

An Yi Yunkurin Kashe Firayi Ministan Iraki

16:42 - November 07, 2021
Lambar Labari: 3486523
Tehran (IQNA) Firayi ministan Iraki ya tsallake rijiya da baya biyo bayan wani hari da aka kai masa a jiya a gidansa a birnin Bagadaza.

Moustafa al-Kazimi Firayi ministan Iraki ya tsallake rijiya da baya a wani harin jirgi marar matuki da aka kai kan gidansa dake yankin Greeen zone a Badagaza a cikin daren jiya wayewar wannan safiya ta Lahadi, kamar yadda Ofishin firaministan ya sanar.
 
Jim kadan bayan firayi ministan ya fitar da wani sako a shafinsa na Twitter, inda yake cewa, ‘’ina cikin koshin lafiya, godiya ga Allah, sannan kuma ina kira ga dukkan bagarori dasu kai zuciya nesa’’
 
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin, sannan ba’a kai ga tantance irin ta’asar da harin ya haifar ba.
 
Kafin hakan dama wasu majoyoyin tsaro sun shaida cewa an kai harin rokoki guda biyu kan gidan firayi ministan Mustafa Al-Kazimi, a yankin mai cikakken tsaro dake tsakiyar babban binrin kasar wan ya kunshi ofishin jakadancin Amurka da kuma gine gine na gwamnati.
 
Bayanai daga kasar sun ce an baza jami’an tsaro a haraba da kuma gewayen inda lamarin ya faru, kamar yadda kuma ake tsaurara matakan tsaro a cikin yankin wanda akasarin manyan jami'an gwamnati a nan suke rayuwa.
 
Bangarori daban-daban na duniya sun yi Allawadai da harin, da hakan ya hada da kasashen duniya gami da kungiyoyi na kasa da kasa, yayin da kasar Iran kuma ta bayyana cewa yunkuri ne na neman haddasa wata sabuwar fitina a cikin kasar Iraki, wanda makiyan kasar suke kitsawa daga wajen kasar.
 

 

4011160

 

captcha