IQNA

Iran Ta Yi Allawadai Da Yunkurin Kisan Firayi Ministan Iraki

23:36 - November 07, 2021
Lambar Labari: 3486526
Tehran (IQNA) Iran ta yi Allawadai da kakkausar murya kan yunkurin kisan firayi ministan kasar Iraki da aka yi a daren jiya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Saeed Khatibzadeh ya bayyana cewa, Iran ta yi Allawadai da kakkausar murya kan yunkurin kisan firayi ministan kasar Iraki Mustafa Alkazimi da aka yi wanda bai yi nasara ba.

Ya ce suna yin kira ga kowa da kowa a Iraki, da su san irin makirce-makircen da ake kullawa kasarsu ta bangarori daban-daban, yana mai cewa irin wadannan abubuwan suna da amfani ga bangarorin da ke tabbatar da zaman lafiya, tsaro, 'yancin kai da kuma 'yancin kasar Iraki cikin shekaru 18 da suka gabata.
 
Ya ce wadanda suka kai harin sun yi hakan ne da nufin cimma bakaken manufofinsu a kasar Iraki, ta hanyar tayar da zaune tsaye, wanda kuma kafin wannan lokacin ma sun yi hakan ta wasu hanyoyi na daban, da suka hada da kirkiro kungiyoyin 'yan ta'adda tare da tura su Iraki suna kai hare-hare kamar yadda duniya ta san da hakan da kuma abin da ya faru.
 

4011309

 

captcha