Jaridar ra'ayul Yaum ta bayar da rahoton cewa, babban shehin cibiyar Azhar ya yi suka kan yadda ake yin amfani da kalmar addinan Annabi Ibrahim a kan addinai na muslunci, kiristanci da kuma yahudanci.
Ya kara da cewa: “Ko da yake a bayyane hakan kira ne zuwa ga hadin kan al’ummar bil’adama, hadin kai da kuma kawar da abubuwan da ke haifar da rikice-rikice, amma a hakikanin gaskiya wannan kira ne wanda bai dace da yin amfani da wannan kalma ba.
" Al-Tayyib ya yi nuni da cewa: Dukkan wannan ‘yancin addini na tauhidi ne ya tabbatar da su, kuma nassosi ma a fayyace sun jaddada su.
A haƙiƙa, irin waɗannan kiraye-kirayen abu ne mai kyau kuma wajibi ne a karfafa hakan a tsakanin al'ummmi da addinai, amma yana da kyau kowane addini a kira shi da sunansa, domin fayyace komai ga mabiyansa, da kuma sanya makiya hadin kan bi adama su yanke kauna.
Sheikh Al-Azhar ya yi nuni da cewa: “Ta hanyar imaninmu da ayyukanmu, mun yi imani da cewa haduwar mutane a kan addini guda ko kuma wata manufa guda ta addinan da aka saukar daga sama, ba zai taba yiwuwa ba, amma dai za a iya fahimtar juna, kuma za a iya yin aiki tare da juna da kuma hadin kai da zaman lafiya, gami da taimakekeniya a tsakanin dukkanin mabiya addinai, da ma bil adam adama baki daya.