IQNA

An Nuna Wani Kur'ani Da Aka Rubuta Da Zinari A Baje Kolin Sharjah

16:12 - November 13, 2021
Lambar Labari: 3486550
Tehran (IQNA) An nuna kur'ani mai tsarki da aka rubuta da zinare tun karni na 12 a wajen baje kolin na Sharjah a Hadaddiyar Daular Larabawa.
Shafin jaridar Araya ya bayar da rahoton cewa, wasu tsoffin fitillun na zamunna da suka gabata, da tsoffin rubuce-rubucen na daga cikin abubuwan da aka kawo a baje kolin littafai na Sharjah karo na 40, wadanda suka ja hankalin maziyarta a wurin baje kolin.
 
Littattafai masu sanya annashawa da tsoffin rubuce-rubucen an ajiye su a cikin wuri na musamman da aka kayata ta shi a cikin gilashi, saboda babban matsayi da wadannan abubuwa suke da shi ta fuskar tarihin addini da kuma adabi.
 
A cewar wani mawallafi, rumfar ta ja hankalin ɗimbin maziyartan baje kolin, waɗanda ke da sha'awar gani da ɗaukar hotuna na tunawa da abubuwan da ba kasafai ake samunsu  ba, kuma masu daraja, wasu daga cikinsu an nuna wa jama'a su ne a karon farko.
 
Fitattun ayyuka dai sun hada da kwafin kur’ani mai tsarki da aka rubuta da zinari carat 24 wanda aka yi tun karni na sha biyu, kuma kudinsa ya kai Yuro 500,000 akalla.

 

4012656

 

captcha