IQNA

Seif Al-Islam Ghaddafi Ya Mika Takardun Neman Tsayawa Takarar Shugabancin Kasar Libya

21:09 - November 15, 2021
Lambar Labari: 3486561
Tehran (IQNA) Seif Al-Islam Ghaddafi ya ajiye takardun takararsa a zaben shugabancin kasar na watan Disamba dake tafe.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, dan tsohon shugaban kasar Libiya, Muammar Ghaddafi, Seif Al-Islam, ya ajiye takardun takararsa a zaben shugabancin kasar na watan Disamba dake tafe.

Seif al-Islam, wanda ya yi shigar tufafi irinta mahaifinsa, mirigayi Muammar Al Kaddafi ya mika takardun takararsa a hukumance ga hukumar zaben kasar ta Libiya a yankin Sebha dake kudancin kasar a wannan Lahadi.

Wannan shi ne karon farko, da Seif Islam, ya fito bainar jama’a.

Zaben shugaban kasar ta Libiya na watan Disamba, wanda ke samun goyan bayan MDD, ana fatan zai kawo karshen yakin da kasar ta fada tun bayan guguwar neman sauyin da ta yi awan gaba da mulkin tsohon shugaban kasar mirigayi Mua’ammar Ghaddafi wanda kuma aka kashe a cikin shekarar 2011.

Saïf Al-Islam, wanda ‘yan bindiga suka kame a watan Nuwamba na 2011, a yankin Zantan, dake arewa maso yammacin Libiya, amma su sallame shi a 2017, bayan da suka ki mika shi ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya dake nemansa bisa zargin laifukan cin zarafin dan adam, saidai daga lokacin ba’a sake jin duriyarsa ba.

 

4013490

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha