IQNA

Cibiyoyin Horar Da Malaman Kur'ani Za Su Ci Gaba Da Ayyukansu A Masar

19:59 - November 19, 2021
Lambar Labari: 3486580
Tehran (IQNA) za a sake bude cibiyoyin al'adu da na horar da masu haddar kur'ani a kasar bayan shafe tsawon shekara daya suna rufe.

Ma'aikatar kula da harkokin kyauta ta kasar Masar ta sanar da shirin sake bude cibiyoyin al'adu da na horar da masu haddar kur'ani a kasar bayan shafe tsawon shekara daya da dakatar da ayyukansu saboda yaduwar cutar korona.
 
Shafin yada labarai na Bawwabatul Ahram ya bayar da rahoton cewa, Ma'aikatar kula da harkokin addini  ta kasar Masar ta sanar a cikin wata sanarwa cewa, a ranar 1 ga watan Disamba za a ci gaba da gudanar da ayyukan cibiyoyin al'adu da na horar da malaman haddar kur'ani a kasar Masar.
 
Sanarwar ta ce: "Za a fara aikin sake farfado da wadannan cibiyoyi saboda rawar da suke takawa a fagen ilimi da wayar da kan jama'a wajen bunkasa matsakaicin tunani da kuma gyara kuskuren fahimta, a ranar 1 ga watan Disamba."
 
Ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar, ta bayyana cewa an dakatar da ayyukan wadannan cibiyoyi tsawon shekara guda sakamakon bullar cutar Corona, ta ce: “Wadannan cibiyoyi suna  hade ne da na haddar kur’ani da koyar da ma’anonin sa. "
 

4014419

 

captcha