IQNA

Iran Ta Bayar Da Kyautar Kwafin Kur'anai Da Littafai Na Addini Ga Wasu Makarantun Addini A Uganda

16:39 - November 21, 2021
Lambar Labari: 3486585
Tehran (IQNA) Iran ta bayar da kyautar kwafin kur'anai da kuma littafai na addini ga makarantun musulmi a yankin Jinja na kasar Uganda.

A yayin zagayowar ranar Allameh Tabatabai da makon littafai,  litattafai masu yawa ne da suka shafi addini, al'adu, tarihi, a matakai daban-daban na matasa da manya, aka bayar a matsayin gudunmawa ga makarantun Islamiyya a Uganda.

Daga cikin littafan akwai mujalladai na fassarar littafan Shahid Morteza Motahhari a cikin harshen mutanen Uganda, da kuma littafan addu'o'i da aka fassara cikin harshen mutanen kasar.

Duk wannan yana daga cikin kyautukan da cibiyar yada al'adu da ilimin musulunci ta kasar Iran ta dauki nauyin bayarwa ga wadannan makarantu.

Kasar Iran dai tana da kyakkayawar dangantaka da kasar Uganda, kamar yadda kuma musulmin kasar suke da kyakkyawar alaka da kasar Iran, wadda take taimaka musu a bangarori daban-daban, musamman wajen gina masallatai da cibiyoyi da makarantu na addini har da na boko.

 

4015094

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar Uganda ، musulmi ، kyautuka ، kyakkyawar alaka ، masallatai ، littafai
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha