IQNA

Kungiyar Bayar Da Agaji ta Musulmi A Burtaniya Ta Kara Fadada Ayyukanta Zuwa wajen Kasar

15:02 - November 23, 2021
Lambar Labari: 3486594
Tehran (IQNA) kungiyar Muslim Hands tana kara fadada ayyukanta a ciki da wajen Burtaniya.
Sadaka da taimakon nakasassu a cikin al'umma da ke fama da matsalar kudi na daga cikin abubuwan da da kungiyar Muslim Hands ta Burtaniya take mayar da hankali a kansu.
 
Yawancin kungiyoyin agaji sun fi mayar da hankali ne kan rage radadin talauci da taimakon kudi da abinci ga talakawa, amma ayyukan wannan kungiya bai takaita ga taimakon tattalin arziki ba.
 
Duk da cewa yana daga cikin manufofin kungiyar agaji rage radadin talauci a tsakanin al’umma, don haka take taika ma mutane ta hanyar ilimi da koyon fasahohi daban-daban, domin su samu abin da za su dogara da shi wajen tafiyar da rayuwarsu.
 
Wannan kungiya ta musulmi tana da babban tasiri a kasar Burtaniya, sakamakon ayyukan alhairi da take gunarwa, inda kuma taimakonta bai takaita ga mabiya addinin musulunci ba, tana taimaka ma kowa mabukaci, ba tare da la'akari da addininsa ko akidarsa ko kabilarsa ko launin fatarsa ba.
 
A lokutan idin musulunci tana bayar da taimako ga iyalai marasa karfi daga cikin musulmi domin su samu damar yin sallar idi cikin farin ciki.
 
Haka nan kuma a lokacin kullen cutar corona, kungiyar ta bayar da gagarumar gudunmawa wajen taimaka ma mutane, musamman marasa karfi da kullen ya cutar da rayuwarsu.
 
 
Abubuwan Da Ya Shafa: taimakon kudi ، agaji ، fasahohi ، mayar da hankali
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha