Shafin yada labarai na Alkafil ya bayar da rahoton cewa, an fara aiwatar da wani shiri an karatun kur'ani mai tsarki a hubbaren Abbas a birnin Karbala tare da halartar makaranta da mahardata.
Wannan shiri dai yana samun halartar makaranta na ciki da wajen kasar Iraki, da hakan ya hada har da baki masu ziyara da suke ziyartar wurare masu tsarki na kasar.
An fara aiwatar da wanann shiri ne tun a shekarun da suka gabata, amma a halin yanzu yana samun bunkasa da karbuwa a tsakanin jama'a.
A halain yanzu baya ga karatu, wasu daga cikin malamai suna gabatar da bayanaia irin wanann majalisi akan ilmomi da suka shafi kur'ani, da kuma wasu darussa da suke cikin ayoyin da ake karantawa.