IQNA

22:59 - November 30, 2021
Lambar Labari: 3486626
Tehran (IQNA) kungiyar kasashen musulmi ta OIC za ta gudanar da zaman taro domin duba halin da ake ciki a kasar Afghanistan.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, kungiyar kasashen musulmi ta OIC za ta gudanar da zaman taro domin duba halin da ake ciki a kasar Afghanistan, bayan da gwamnatin kasar Saudiyya ta bukaci hakan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-Sharq Al-Awsat cewa, jami'an kasar Saudiyya na cewa, a bisa tsarin hadin kan musulmi tana ganin ya zama wajibi ta gudanar da wani zama na musamman na majalisar ministocin kasashen musulmi domin tattaunawa kan halin da ake ciki a kasar ta Afganistan, da kuma taimakawa kasar wajen ayyukan  jin kai da ya dace.
 
Riyadh ta jaddada cewa, tana fatan taron da Jamhuriyar ta Pakistan za ta dauki bakuncinsa a ranar 17 ga Disamba,  don taimakawa wajen samar da hanyoyin da suka dace domin taimakon al'ummar Afganistan, ya zama wata hanya ta samun sauki ga al'ummar kasar.
 
Za a gudanar da taron ne tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya, hukumomin da abin ya shafa, cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa da kasashen duniya don rage tasirin rikicin matsalolin da al'ummar Afghanistan.ke ciki.
 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: