IQNA

Saudiyya Ta Sake Bude Karamin Ofishin Jakadancinta A Afghanistan

15:56 - December 01, 2021
Lambar Labari: 3486628
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Saudiyya ta sake bude karamin ofishin jakadancinta a birnin Kabul na kasar Afghanistan.
Gwamnatin kasar Saudiya ta bada sanarwan cewa a jiya Talata ta sake bude karamin ofishin jakadancinta da ke birnin Kabul babban birnin kasar Afgansitan don gabatar da hidimomi ga mutanen kasar.
 
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto kafafen yada labarai na kasar ta Saudiya da dama suna bada labarin sake bude karamin ofishin jakadancin kasar da ke birnin Kabul babban birnin kasar ta Afganistan.
 
Kafin haka dai Saudiya da wasu kasashen yamma da dama sun rufe ofisoshin jakadancinsu da ke Kabul a cikin watan Agustan da ya gabata a dai dai lokacinda kungiyar Taliban ta sake dawowa kan madafun iko a kasar.
 
Amurka ta mamaye kasar Afganistan a cikin shekara ta 2001 ta kuma kori gwamnatin Taliban daga madafun ikn kasar, sannan wannan halin ya ci gaba har na tsawon shekaru 20 ba tare da zaman lafiya ta dawo kasar ba.
 
Bayan kissan sojojinta masu yawa ga kuma miliyoyin dalar Amurka ta take kashewa a duk ranar Allah Amurka ta fice daga kasar Afganistan a ranar 31 ga watan Augustan da ya gabata. Sannan taliban ta kwace iko daga gwamnatin da kasar Amurkan ta kafa.
 
 
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha