IQNA

Amfani Da Kayayyakin Abincin Halal Tsakanin Wadanda Ba Musulmi Ba Yana Karuwa

19:40 - December 02, 2021
Lambar Labari: 3486634
Tehran (IQNA) Cibiyar kasuwanci da masana'antu ta China-Malaysia ACCCIM ta ba da rahoton karuwar amfani da kayayyakin halal a tsakanin wadanda ba musulmi ba a duniya.

Babban sakataren cibiyar ta hadin gwiwa tsakanin China da Malaysia  Tan Tian Meng ya bayyana cewa, Dalilin wannan karuwar shi ne wadanda ba musulmi ba sun fahimci mahimmancin shaidar halal a matsayin wani bangare na tsarin abinci lafiyayye da aminci idan aka kwatanta da kayayyakin da ba na halal ba.

Ya kara da cewa: Ci gaban da kasuwar halal ta samu a baya-bayan nan ya sauya yanayi da kuma karbuwar kayan abincin Halal a tsakanin wadanda ba musulmi ba a duniya.

Tan ya ce bangaren ayyukan samar da kayan abincin halal na Malaysia, na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da ci gaban tattalin arzikin kasar.

A halin yanzu akwai musulmi kusan biliyan 1.9 a duniya, wadanda ke da kusan kashi 26% na al'ummar duniya, wanda kuma wannan adadi yana nuni da cewa musulmi suna da babban tasiri a cikin harkokin tattalin arziki na duniya.

 

4017748

 

captcha