
Kafofin yada labaran Falastinu sun bayar da rahotannin cewa, fiye da Falasdinawan 45,000 ne suka gudanar da sallar Juma'a a harabar masallacin Al-Aqsa a daidai lokacin da gwamnatin yahudawan sahyuniya ke daukar matakan tsaro.
Da sanyin safiyar yau ne dubun dubatar Falasdinawa mazauna Yammacin Kogin Jordan da yankunan da aka mamaye suka isa masallacin Al-Aqsa domin gabatar da sallar Juma'a.
Sheikh Mohammad Sarandah limamin masallacin Al-Aqsa a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma'a ga al'ummar Palastinu ya ce, a ko da yaushe yana shelanta cewa, masu kula wannan masallaci za su samu kyakkyawan sakamako a gobe kiyama, saboda babban jihadin da suke wajen kare wannan harami mai alfarma.
Sheikh Mohammed Sarandah ya kuma yaba da kasancewar dalibai da malaman Falasdinawa a kullum a masallacin Al-Aqsa, domin tabbatar wa yahudawa cewa wannan wuri mallaki na al'ummar musulmi.
https://iqna.ir/fa/news/4018106