IQNA

14:36 - December 04, 2021
Lambar Labari: 3486639
Tehran (IQNA) Wani mutum mai suna Ibrahim Ahmad Nawwar yana ajiye da wani tsohon kur’ani wanda kuam shi ne mafi karanta a kasar Jordan.

Ibrahim Ahmed Nawar, mai shekaru 62, wanda ke zaune a birnin Al-Salt na kasar Jordan, ya kafa wani gidan tarihi mai zaman kansa mai suna The Permanent Museum of National Heritage.

A cikin wannan gidan kayan gargajiya, tare da wurare masu sauƙi, yana adana fiye da 25,000 ayyuka masu mahimmanci na fasaha, yawancin su sun kasance a farkon karni na ashirin.

Daga cikin abubuwan da yake adanawa har da Kur’ani mafi kankanta a duniya wanda tsawonsa ya kai cm 2.5 da fadinsa cm 1.5.

A wata hira da ya yi da Anatoly, Ibrahim Ahmad Nawar ya ce: "Masana da kwararru bayan sun ziyarci wannan kur'ani, sun sanar da cewa wannan sigar ita ce mafi kankantar kur'ani da aka buga a duniya."

Wannan mutum dan kasar Jordan ya karbi wannan kur'ani a shekarar 1980 daga wani mazaunin birnin Al-Salt, wanda shi ma ya gaji wannan aiki mai daraja daga mahaifinsa.

Wasu masana sun yi kiyasin cewa wannan bugu na kur'ani da aka buga ya wuce shekaru 100, tun farkon karni na ashirin.

 

‌نگه‌داری کوچک‌ترین قرآن چاپی جهان در موزه اردن

‌نگه‌داری کوچک‌ترین قرآن چاپی جهان در موزه اردن

‌نگه‌داری کوچک‌ترین قرآن چاپی جهان در موزه اردن

4018041

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: