IQNA

Kungiyoyin Farar Hula A Malaysia Na Goyon Bayan Iran A Tattaunawar Nukukiliya

20:23 - December 05, 2021
Lambar Labari: 3486646
Tehran (IQNA) Gamayyar kungiyoyin farar hula a kasar Malaysia ta sanar da cikakken goyon bayanta ga kasar Irana tattaunawar nukiliya.

A cikin wani bayani da ta fitar ga manema labarai a yau a birnin Kuala lumpur, Gamayyar kungiyoyin farar hula a kasar Malaysia ta bayyana matsayarta dangane da matsayar Amurka a tattaunawar nukiliya da Iran, inda sanar da goyon bayanta ga kasar ta Iran.
 
Bayanin ya ce, irin yadda Amurka ta dauki matakin ficewa daga wannan yarjejeniya tun daga farko, ya tabbatar da cewa ba da gaske take yi ba, bil hasali ga dukkanin alamu manufarta ita ce rushe yarjejeniyar baki daya saboda dalilai na siyasa.
 
Haka nan kuma bayanin ya ishara da matsayar Amurka a wanann tattaunawar zagaye na bakwai da aka bude a makon da ya gabata, inda kungiyar ta ce Amurka na neman yi wa tattaunawar wata sabuwar kutunguila, kmar yadda kuma kungiyar ta ce tana mara baya ga matsayar da Iran kan matsayar da ta dauka na neman hakkokinta ba tare da wani tsoro ba.
 
 

4018435

 

captcha