IQNA

Ana Fargaba Kan Yiwuwar A Rushewar Babban Masallacin Tarihi Na Cordoba A Spain

22:35 - December 06, 2021
Lambar Labari: 3486649
Tehran (IQNA) ana nuna fargaba matuka kan yiwuwar rushewar masallacin Cordoba na tarihi da ke kasar Spain.

Jaridar Times ta kasar Ingila ta bayar da rahoton cewa, rahoton da aka mika wa gwamnatin kasar Spain a wannan mako na barazanar ruguza babban masallacin Crdoba saboda miliyoyin 'yan yawon bude ido da ke ziyartarsa ​​a duk shekara.

An gina masallacin ne a wajen wani tsohon coci da ke a matsayin babban coci tun bayan da dakarun Kirista suka koma birnin wanda ke kudancin Spain a shekara ta 1236, kuma yanzu haka yana da maziyarta kusan miliyan biyu a kowace shekara.
محراب مسجد جامع قرطبه

Rahoton ya ce cunkoson maziyartan ya haifar da barna mai yawa a sassa daban-daban na masallacin, ciki har da bagayen masallacin.
 
Abin tuni a nan dai shi ne cewa, bayan bullar cutar Corona, adadin masu ziyartar wannan masallaci ya ragu, amma bayan bude shi a watan Afrilun bana, wannan tsohon wurin tarihi ya shaida zuwan maziyarta 53,000 a watan Mayun 2021 kadai.
 
Wannan hatsarin yana karuwa kowace rana saboda birnin Cordoba shi ne birni mafi zafi a yankin Iberian, kuma a lokacin rani yanayin zafi a wannan birni ya kan kai kimanin daraja 47 a ma'aunin celcius. 
 
Don haka ma'aunin zafi na muhalli yana da yawa kuma yana da haɗarin lalata wasu kayan da ake adana su a wurin, wanda hakan yasa hukumar kula da kayan tarihi ta kasar Spain ta fara tunanin daukar matakan da suka dace domin kubutar da wannan masallaci mai tsohon tarihi, da sauran kayan tarihin da suke a wurin.
مسجد جامع قرطبه در اسپانیا
گنبد مسجد جامع قرطبه
 

4018626

 

Abubuwan Da Ya Shafa: shekara ، masallaci ، miliyoyin ، yawon bude ido ، masallacin Crdoba
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha