IQNA

Hamas Ta Jinjina Wa Kuwait Kan Matsayin Da Ta Dauka Kan isra'ila

23:28 - December 06, 2021
Lambar Labari: 3486651
Tehran (IQNA) kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta yi maraba da matakin da Kuwait da dauka kan Isra'ila.

Tashar TRT ta bayar da rahoton cewa, kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta yi maraba da matakin da Kuwait da dauka kan Isra'ila.

Shugaban bangaren yada labarai na kungiyar ta Hamas Hisham Qasim ya ce "Wannan mataki na nuni da aiwatar da tsohuwar da kuma sabuwar manufar kasar Kuwait, wanda a ko da yaushe ya ginu ne a kan kare Falasdinu da manufofi na adalci."
 
Ya ci gaba da cewa: Wannan shawarar ta tabbatar da ra'ayin kungiyar Hamas, wadda a ko da yaushe ta yi imani da cewa, ya zuwa yanzu, duk da yanayin da ake ciki na hankoron daidaita alaka da Isra'ila da wasu daga cikin larabawa  da ke yi, amma har yanzu al'ummar musulmi suna goyon bayan al'ummar Falastinu.
 
Wakilin na Hamas ya yi kira ga kasashen Larabawa, da na musulmi da abokan kawance da su bi matakin da Kuwait ta dauka na haramtawa 'yan mamaya amfani da tashar jiragen ruwansu wajen shigo da kayansu ko fitar da su, a daidai yahudawan Isra'ila 'yan mamaya ke ci gaba da kashe Falasdinawa da kwace filayensu da kuma tozarta wurare masu tsarki na al'ummar musulmi.
 
Kasar Kuwait ta dauki matakin adawa da daidaita alaka da Isra’ila, kuma jami’anta a kodayaushe suna nuna goyon bayansu ga al’ummar Palastinu tare da yin watsi da duk wani batu na daidaita alaka da Isra’ila.
 

 

4018639

 

Abubuwan Da Ya Shafa: hamas maraba gwagwarmaya kungiyar dauka
captcha