Shafin yada labarai na Alwafd ya bayar da rahoton cewa, Mutanen da ke da larurua ta musamman masu himma da jajircewa za su ci gaba da fafatawa a rana ta biyu ta gasar kur'ani ta kasa da kasa ta Masar.
Wannan gasa ta kunshi bangarori daban-daban, musamman ganin cewa akwai masu lalrura ta musamman da suke da banbance-banbance wajen gudanar da gasar, domin kuwa ba a takaitu ga fasahar haddar ba.
Akwai abubuwa kamar sautin kur’ani da sauti da furuci da kuma wasu abubuwa na musamman kamar haddar lambobin shafi da ayoyi a cikin wannan gasa, wanda suma masu larura ta musamman za su taka rawar gani a wadannan fannoni.