IQNA

Ministan Addini A Masar: Masu Tsattsauran Ra'ayi Da Ke Aikata Ta'addanci Ba Su Wakiltar Musulunci

22:44 - December 13, 2021
Lambar Labari: 3486681
Tehran (IQNA) Yayin da yake gabatar da wata zantawa da wani gidan talabijin a jiya ministan ma’aikatar kula da harkokin addini na Masar, ya jaddada cewa Musulunci ya barranta daga kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi.

Ministan  ma’aikatar kula da harkokin addini na Masar Mohammed Mukhtar Juma a daren jiya Lahadi 12 ga watan Disamba a wata hira ta wayar tarho da shirin "Sabuwar Masar" da aka watsa a tashar ETC, ya bayyana cewa kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi suna aikata laifuka karkashin tutar Musulunci da Kur'ani domin cimma burinsu.

Ya ce abin da suke yi ya yi hannun riga da koyarwar addinin musulunci, kamar yadda kuma ya yi kashedin cewa, abin suke yi yana bata sunan addinin musulunci, saboda dole ne malamai su kalubalanci irin wannan mummunar akida.

Dangane da gasar kur'ani ta duniya da ke gudana a yanzu akasar Masar kuwa, ya bayyana cewa sun kyakkyawan shiri dangane ad gasar, domin tabbatar da cewa komai ya tafi kamar yadda aka tsara.

Kamar yadda ya yi fatan alhairi ga dukkanin mahalarta wannan gasa da suka zo daga kasashe na duniya, da fatan kuma za a gudanar komai lafiya a kare lafiya.

 

 
 
 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ministan ، kashedin ، daren jiya ، koyarwar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha