IQNA

An bayyana sunayen wadanda suka lashe gasar kur'ani ta kasa da kasa a Masar

15:53 - December 16, 2021
Lambar Labari: 3486690
Tehran (IQNA) Ma'aikatar kula da harkokin addini ta Masar ta sanar da sunayen wadanda suka lashe gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa karo na 28.

A cewar Ma'aikatar kula da harkokin addini ta Masar, a rukunin farko na gasar da ta hada da "hardar kur'ani cikakke tare da karatun kur'ani da fahimtar ma'anonin ayoyin kur'ani" ga mahalarta masu magana da harshen larabci "Abdullah Ali Muhammad Mohammed." " daga Masar, "Sara Ayman Ahmad Musa" daga Masar, Iman Jamal Farooq Hassan na Masar da Abdul Hamid Abdullah Omar na Libya sun zo na daya zuwa na hudu.

A rukuni  na biyu na gasar da ta hada da "hardar kur'ani cikakke tare da Tajweed" ga wadanda ba sa jin harshen Larabci, "Abu Bakr Teshmala" na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, "Mohammad Ali Shanfi" daga tsibirin Comoros "Abdul Rahman Saleh" daga Najeriya, "Ali Atiya Ibrahim" daga kasar Chadi da kuma "Isma'il Drama" na Ivory Coast sun zo na daya zuwa na biyar.

Rukuni na uku na gasar dai ya hada da "hardar kur'ani ga masu bukata ta musamman  "Nadi Saad Jaber Mohammad" da "Mohammad Ahmad Hassan Abdul Abdul Halim", "Abdul Rahman Mehdi Jamal Ahmad", "Ahmad Mohammad Mohammad" Ali Al-Sayed” da “Amir Ahmad Abdul Wahab Mohammad” dukkansu sun fito ne daga kasar Masar, a matsayi na daya zuwa na biyar.

Har ila yau, a rukuni na hudu na wannan gasa da ta hada da "Hardar  kur'ani Mai Girma da Tajwidi" ga matasa "Shirin Mohammad Abdullah Amin", "Ahmad Tamer Mamdouh Mohammad Sabri", "Rumisa Ahmad Ibrahim Abdul Ati" da "Mustafa Al- Sayed Nasr Abdul Salam" Dukkaninsu wakilan kasar Masar ne kuma suka samu matsayi na daya zuwa hudu.

Rukuni na biyar na gasar "hardar kur'ani cikakke tare da karatun tafsiri”  "Ayman Mansour Abdul Aziz" na kasar Masar, "Awadullah Al-Tayyib Ahmad" daga Sudan, "Ahmad Mehdi Mustafa Mehdi" daga Masar, "Mohammad Hassan Abdul Azim Hassan na Masar da Mohammed Tariq Ansari na Indiya a matsayi na daya zuwa na biyar.

A ranar Asabar 11 ga watan Disamba ne aka fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa karo na 28 a kasar Masar, inda aka samu halartar dimbin malaman kur’ani daga kasashen duniya daban-daban a bangaren maza da mata.

Ma'aikatar kula da harkokin addini ta Masar ce ta shirya wadannan gasa da sunan  marigayi "Sheikh Mohammed Siddiq Al-Manshawi", daya daga cikin fitattun makarata kuma mahardata na Masar.

Gasar ta samu halartar mahalarta 74 daga kasashe daban-daban na duniya da alkalai 12 na kasa da kasa daga ciki da wajen Masar da suka yi alkalanci a wadannan gasa, sannan kuma aka bayar da kyautuka na kusan fam miliyan daya da dubu 100 na Masar (daidai da dala dubu 67) ga wadanda suka yi nasara.

Haka nan kuma an sami 140,000 (kimanin $ 9,000) cikin kyaututtukan ƙarfafa gwiwa ga waɗanda ke da maki kasa da 75%.

 

4021294

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: gasar kur’ani ، kasar Masar ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha