IQNA

Dubban Musulmin Rohingya 'Yan Gudun Hijira Na Fuskantar Matsalar Rashin Samun Ilimi

19:51 - December 21, 2021
Lambar Labari: 3486711
Tehran (IQNA) Dubban 'yan kabilar Rohingya masu neman mafaka na fuskantar matsalar hana su samun ilimi sakamakon rufe makarantu a yankin Cox's Bazar da gwamnatin Bangladesh ta yi.

Shafin yada labarai na Alwafd ya bayar da rahoton cewa, rayuwar Musulman Rohingya na ci gaba da tabarbarewar duk da kiraye-kirayen da kasashen duniya suka yi na a kawo karshen wahalhalun da wadannan masu neman mafaka suke ciki.

Kungiyoyin kasa da kasa sun soki matakin baya-bayan nan da gwamnatin Bangladesh ta dauka a sansanonin 'yan gudun hijira Musulman Rohingya.
 
Bangladesh ta yanke shawarar rufe makarantu a sansanonin Cox's Bazar, matakin da zai hana dubban 'yan gudun hijira samun ilimi. Hukumomin kasa da kasa sun yi gargadin illar da irin wannan hukunci zai haifar.
 
Duk da cewa Bangladesh ta taka muhimmiyar rawa wajen ceto 'yan gudun hijirar Rohingya musamman bayan zaluncin da aka yi musu a shekarar 2017 a kasarsu ta Myanmar, inda gwamnatin Bangaladesh ta dauki matakin tsugunnar da su a cikin kasarta, duk da cewa da ta hana shigar 'yan gudun hijirar a cikin kasarta, amma matakan baya-bayan da take dauka a kansu sun yi hannun riga da hakkokinsu, daga cikin waɗannan matakan har da hana yaran Rohingya shiga makarantun gwamnati da kuma makarantu masu zaman kansu, da kuma taƙaita shirye-shiryen ilimi da ƙungiyoyi masu zaman kansu ke bayarwa a sansanoninsu.
 
Sai dai kuma da dama daga cikin kungiyoyin kasa da kasa musamman kungiyoyin addinin Islama sun jaddada wajabcin samar da rayuwa mai aminci da mutuntawa ga Musulman Rohingya, kuma sun yi la'akari da cewa 'ya'yansu na da damar samun isasshen ilimin da ya dace, bisa la'akari da hakkokinsu na  addini da kuma hakkokinsu na kasa da kasa a matsayinsu na bil adama.
 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kungiyoyin addinin Islama ، Musulman Rohingya ، bil adama ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha