IQNA

An Daure Wani Musulmi Watanni 8 A Faransa Saboda Yin Kabbara A Wata Kasuwa

23:47 - December 22, 2021
Lambar Labari: 3486717
Tehran (IQNA) wata kotu a kasar Faransa ta yankewa wani musulmi dan kasar hukuncin daurin watanni 8 a gidan yari sakamakon yin kabbara da karfi a wani wurin hada-hadar kasuwanci.
Kotun ta ce ta samu mutumin dan wata kungiyar Islama mai tsattsauran ra'ayi da laifin yin kabbara da karfi a tsakiyar jama'a a cikin wuri na kasuwanci, a kan haka ta yanke masa hukuncin daurin watanni takwas a gidan yari saboda ya haddasa firgici a tsakanin jama'a.
 
An kuma ci tarar mutumin mai shekaru 52 € 750 da kuma yanke masa hukuncin shekaru biyu na rashin shiga cikin jama'a, Sai dai kuma an wanke abokin tafiyarsa mai shekaru 38 daga tuhumar da ake masa.
 
Mutumin ya shaida wa kotun cewa: “Ya yi matukar farin ciki da jin labarin bude cibiyoyin addini a arewacin kasar Faransa, da kawo karshen takurar da ake yi wa jama'a da ke alakantawa da barkewar cutar korona, saboda haka ya yi kabbara ne sabo da jin dadin wannan labari da aka ba shi.
 
Ya ce: "Babu wata niyya da yake da ita tsoratarwa ko tayar da hankalin jama'a sakamakon kabbarar da ya yi.
 
Wani mai magana da yawun babban mai shigar da kara, ya bayyana cewa an taba samun mutumin da laifin firgita jama'a a wata coci a birnin Lyon a lokacin jana'iza a cikin watan Disamban 2016, lamarin da yasa mutane suka yi ta ficewa daga cocin a firgice.
 
https://iqna.ir/fa/news/4022678
Abubuwan Da Ya Shafa: wata kotu ، kasar Faransa ، mutane ، kabbara ، niyya ، babban mai shigar da kara
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha