IQNA

Shugaban Ofishin Jagoran Juyi Na Iran A Ingila Ya Aike Wa Kiristoci Da Sakon Taya Murnar Kirsimati

19:08 - December 25, 2021
Lambar Labari: 3486725
Tehran (IQNA) wakilin Jagoran juyin Musulunci na Iran a Ingila ya taya daukacin mabiya addinin kirista murnar zagayowar lokacin kirsimati da sabuwar shekarar miladiyya.

A cikin sakon da ya aike dangane da zagayowar lokacin haihuwar Annabi Isa (AS) da kuma sabuwar shekarar miladiyya, wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Iran a Ingila Sayyid Hashem Mousavi ya taya daukacin mabiya addinin kirista murnar zagayowar wannan lokaci.

A cikin sakon wakilin jagoran juyin na kasar Iran ya bayyana cewa, batun haihuwar annabi Isa (AS) lamari ne na ubangiji wanda yake cike da ayoyinsa masu girma, kama tun daga haihuwarsa a cikin kankanin lokaci a cikin ikon ubangiji, da kuma kalaman da ya yi jim kadan bayan haihuwarsa, da kuma abubuwan da suka kasance tare da shi a cikin tsawon lokacin da ya dauka tun daga kuruciya har zuwa aiko da annabta.

Ya ci gaba da cewa, lamarin Anabi Isa (AS) na dukkanin mabiya addinai ne da aka saukar daga sama, domin kuwa addinin da ya zo da shi daga Allah ne, na tsakake Allah da kuma kadaita shi a cikin bauata, kamar yadda sauran annabawan Allah amincin Allah ya tabbata a gare su suka yi.

Daga karshe ya ina roqon Ubangiji Madaukakin Sarki da Ya sa wannan sabuwar shekara ta zama shekara mai cike da farin ciki da lafiya ga dukkanin al'ummomi na duniya, ya kuma kawar mana da sharrin wannan cuta da ta addabi al'ummomin duniya, ya kuma maimaita mana shekaru masu a cikin alhairi da albarka.

 

 

4023327

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: shekaru maimaita mana cuta da ta addabi
captcha