IQNA

Musulmin Kasar Burtaniya Sun Mika Sakon Ta'aziyyar Rasuwar Desmond Tutu

15:57 - December 27, 2021
Lambar Labari: 3486736
Tehran (IQNA) musulmin kasar Burtaniya sun mika sakon ta'aziyyar rasuwar marigayi Desmond Tutu daya daga cikin manyan jagororin gwagwarmaya da wariyar launin fata a Afirka ta kudu.

Majalisar musulmin kasar Burtaniya ta fitar da bayanin da ke cewa, Desmond Tutu mutum ne wada tarihi ba zai taba mantawa da shi ba, sakamakon gagarumar gudunmawar da ya bayar a cikin rayuwarsa.

Bayanin ya ce, baya ga gwagwarmaya da wariyar launin fata da ya yi tare da abokinsa Nelson Mandela, ya kuma kasance daga cikin mashahuran mutane a duniya a da suke adawa da zaluncin da Isra'ila take kan al'ummar falastinu, kamar yadda kuma yake goyon dauakr dukkanin matakan da suka dace domin ladabtar da Isra'ila kan zaluntar Falastinawa da take hakkokinsu.

A jiya ne dai Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ne ya sanar da rasuwar ta Desmond Tutu a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya rasu a wani asibiti dake birnin Cape Town a jiya Lahadi yana da shekaru 90 a duniya.

Kasashen duniya da dama da kuma fitattun mutane a duniya suan ci gaba da aikewa da sakon ta'aziyyarsu kan rasuwar Archbishop Desmond Tutu, daya daga cikin mutanen da suka karbi kyautar Nobel ta zaman lafiya.

 

4023817

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha