IQNA

Za A Gudanar Da Taron Jagororin Addinai Kan Zaman A Lokacin Tunawa Da Shahadar Qasim Sulaimani

15:57 - December 29, 2021
Lambar Labari: 3486745
Tehran (IQNA) za a gudanar da taron jagororin addinai a kasar Iran a daidai lokacin tunawa da cikar shekaru biyu da shahadar Qasim Sulaimani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatar kula da harkokin yada al'adu na musulunci a kasar Iran, za ta dauki nauyin gudanar da taron jagororin addinai a kasar a daidai lokacin tunawa da cikar shekaru biyu da shahadar Qasim Sulaimani. 

Bayanin ya ce, taron zai gudana ne a cikin makon farko na watan Janairun shekarar miladiyya mai kamawa, wanda zai samu halartar jagororin addinai na bangarorin musulmi da kiristoci, zartush da sauransu.

Babbar manufar taron dai ita ce karfafa zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai, da kuma kara samun fahimtar juna a zamantakewarsu.

An shirya gudanar da taron nea  lokacin tunawa da shahadar Qasim Sulaimani da Abu Mahdi Almuhandis ne, kasantuwar cewa wadannan manyan gwaraza biyu sun bayar da gudunmawa da hidima mai yawa wajen karfafa wannan tunani, kamar yadda suka taimaka ma mabiya addinai daban-daban a cikin kasashen Iraki da Syria.

Amurka ta aiwatar da kisan gilla a kan wadannan mutane biyu a ranar 1 ga watan janairun shekara ta 2020, bayan da tsohon shugaban kasar Amurka na lokacin Donald Trump ya bayar da umarnin aiwatar da hakan.

 

4024484

 

 

captcha