IQNA

Sheikh Qassem: Hizbullah Za Ta Shiga Zaben 'Yan Majalisar Lebanon Da Karfinta

22:09 - December 30, 2021
Lambar Labari: 3486759
Tehran (IQNA) Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Labanon ya bayyana cewa, Hizbullah za ta shiga zaben Lebanon da karfinta.

Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Labanon ya bayyana cewa: Wannan yunkuri zai taka rawar gani sosai a zaben 'yan majalisar dokoki da za a gudanar a watan Mayun shekara ta 2022, kuma ma'auni na shiga zaben shi ne yi wa al'umma hidima da kuma kare al'umma.

Mataimakin Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sheikh Naeem Qasim ya bayyana a cikin wani jawabi da ya yi cewa kungiyar za ta shiga cikin zabukan 'yan majalisar dokokin kasar da aka shirya gudanarwa a watan Mayun shekarar 2022.

Sheikh Naeem Qasim ya kara da cewa: Wannan zabe shi ne zai wakilci zabin al'umma sannan kuma al'ummar kasar za ta tantance wanda zai yi mata wakilci.

Manufar wannan gasa ita ce kare kasar Labanon daga makiya yahudawan sahyoniya da warware matsalolin da al'ummar kasar ke fuskanta a fannonin tattalin arziki da zamantakewa da kuma kiwon lafiya daban-daban.

Sheikh Naeem Qasim ya ci gaba da cewa: “Mun san cewa akwai kishin kasa da ba a taba ganin irinsa ba a zaben, kuma akwai yunkuri da wasu jam’iyyu ke yi masu adawa da ayyukanmu na kasa, saboda suna ganin cewa wakilai da dama ne za su shiga zaben kuma za su canza wannan daidaito.

Mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya kara da cewa: Yakin neman zabenmu na da karfi da tasiri a makomar kasar da kuma hidimtawa al'umma, wannan shi ne ma'aunin da zai yi tasiri wajen samar da makomar kasar ta Lebanon makoma mai kyau nan da shekaru hudu masu zuwa."

 

 

4024787

 

 

captcha