IQNA

Manyan Alluna Dauke Da Hotunan Janar Kasim Sulaimani A Titunan Zirin Gaza Palestine

21:03 - January 03, 2022
Lambar Labari: 3486776
Tehran (IQNA) a jajibirin cika shekaru biyu da shahadar Qassem Soleimani, ana kafa manyan alluna dauke da hotunansa a titunan zirin Gaza.

A daidai lokacin da ake cika shekaru biyu da shahadar Qassem Soleimani, kwamandan dakarun Quds na dakarun kare juyin juya halin Musulunci a iran, an girka manya-manyan hotunansa a tituna da shataletale daban-daban a Zirin Gaza.
 
Mohammad al-Barim, daraktan ofishin yada labarai na kwamitocin gwagwarmaya na Falasdinawa ya bayyana cewa: "Gaza na tare da Hajj Qassem Soleimani a taron cika shekaru biyu da shahadarsa.
 
Ya ce Gaza ta yi tsayin daka wajen tunkarar 'yan mamaya sakamakon karfin gwiwa da taimakon da Qasim Sulaimani ya baiwa Falastinawa 'yan gwagwarmaya na zirin Gaza ne, saboda haka a cewarsa, Sulaimani babban kwamanda ne na gwagwarmayar Falastinawa.
 
Al-barim ya kara da cewa: A yayin zagayowar ranar shahadar Haj Qasim Soleimani, muna masu jaddada alkawarin daukar fansa kan jininsa, muna kuma jaddada cewa za mu ci gaba da tunawa da shi da kuma bin tafarkinsa da kuma matakan da ya dauka a tafarkin tsayin daka domin 'yantar da al'ummomi da ake zalunta..
 
Kamar yadda kuma ya ce Falastinu ba za ta taba mantawa da kyawawan halayensa ba, da kuma sadaukarwar da ya yi saboda su da kuma nema musu 'yancinsu daga mamayar yahudawa.
نصب تصاویر سردار سلیمانی در خیابان‌ها و میادین غزه
 
نصب تصاویر سردار سلیمانی در خیابان‌ها و میادین غزه

4025471

 

 

 

captcha