IQNA

Bafalastinan Da Ke Yajin Cin Abinci A Kurkukun Isra'ila Bayan Kwashe Kwanaki 141 Ya Samu 'Yancinsa

18:55 - January 05, 2022
Lambar Labari: 3486782
Tehran (IQNA) Bafalastinen da dake yajin cin abinci na tsawon kwanaki 141 a kurkukun Isra'ila ya samu 'yancinsa.
Hisham Abu Hawwash, wanda ya kwashe kwanaki 141 a jere yana yajin cin abinci a kurkukun Isra’ila, ya dakatar da yajin cin abincin nasa bayan da aka cimma matsaya kan sakinsa daga hannun Isra'ila, a cewar majiyoyin Falasdinawa.
 
Hukumar da ke kula da fursunonin Falasdinu a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, Abu Hawwash, wanda ya shiga yajin cin abinci tsawon kwanaki 141 da suka gabata, don nuna adawa da tsare shi ba tare da wani dalili ko wata tuhuma ba, ya kawo karshen yajin cin abincin a daren jiya Talata, bayan cimma wata yarjejeniya, wanda a karkashinta za a sake shi a ranar 26 ga Fabrairu mai kamawa.
 
Sanarwar ta kara da cewa, "Yarjejeniyar ta tanadi sakin Abu Hawash a ranar 26 ga watan Fabrairu ba tare da wani karin wa'adi ba.
 
Shi ma lauyan kungiyar fursunonin Falasdinu (PPS), Jawad Boulos, ya tabbatar da cewa an cimma matsaya, kuma bafalastinan mai shekaru 40 da haihuwa ya janye yajin cin abinci bayan kwashe tsawon kwanaki 141 a jere yana yajin cin abinci.
 
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4026279
captcha