IQNA

Gasar Tantance Makaranta A Masar Zuwa Kasashen Domin Karatun Kur'ani A Watan Ramadan

19:53 - January 06, 2022
Lambar Labari: 3486789
Tehran (IQNA) Ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar na gudanar da gasar tantance masu karatun kur'ani da za atura su kasashen waje a watan Ramadan.

Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, Ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta sanar da gudanar da gasar tantance makaranta da za a tura su karatun kur'ani mai tsarki zuwa kasashen waje a cikin watan Ramadan mai zuwa.

Za a gudanar da wannan gasa ne a tsakanin fitattun malamai daga cikin limamai da masu shirya tarurrukan addini da ma'aikatan cibiyoyin addini da kuma ma'abota karatu na kungiyar masu karatu da kuma fitattun masu karantu a gidajen rediyo da talabijin.
 
 Masu neman shiga gasar dole ne su cika wasu sharudda, kamar gabatar da takardun shedar zama memba a ƙungiyar masu karatu, ko gabatar da karatu a rediyo da talabijin, cin jarrabawar rubuce-rubuce, da kuma shaidar da ke tabbatar da mutum bai taba aikata wani mummunan laifi ba.
 
Ana gudanar da jarrabawar share fage ne a ofisoshi na yankuna, sannan kuma a gudanar da jarrabawar karshe a ofifin babban daraktan ma’aikatar kula da addini.
 
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4026625
captcha