IQNA

Dan Abdul Basit ya ziyarci Majalisar Al-Qur'ani ta Sharjah

19:33 - January 08, 2022
Lambar Labari: 3486792
Tehran (IQNA) Tariq Abdul Basit dan Abdul Basit Mohammed Abdul Samad, fitaccen makarancin kasar Masar, ya ziyarci cibiyar da ke zauren kur'ani na Sharjah da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa tare da sanin sassanta daban-daban.

Halifa Mesbah al-Taniji shugaban majalisar kur'ani ta Sharjah ne ya tarbi wannan ziyara ta Tariq Abdul Basit.

Dan Abdul Basit a cikin wannan ziyarar ya ce: Na yi kokari matuka wajen ziyartar Majalisar Alkur'ani mai girma ta wannan gari a lokacin tafiyata zuwa Sharjah; Wannan hadadden gini ne mai girma da ban sha'awa da kuma nuni ga masana da masu bincike.

Shugaban majalisar makaranta kur’ani Karim Sharjah a lokacin da yake maraba da Tariq Abdul Basit ya ce: “Wannan kungiya wata hasumiya ce wacce masu neman ilimi da masu sha’awar kur’ani za su amfana da ita.

Al-Taniji ya kara da cewa: Majalisar kur'ani mai tsarki ta Sharjah tare da sassanta daban-daban, tana kokarin karfafa hanyoyin bincike da nazarce-nazarcen ilimi, kuma a cikinta akwai ayyuka masu kima da suka shafi shahararrun makaranta na kasashen musulmi.

Bayan kammala taron, babban sakataren majalisar kur'ani mai tsarki ta Sharjah Sheikh Shirzad Abdul Rahman Tahir ya bayyana manufofin majalisar da tsare-tsaren bincike ga Tariq Abdul Basit.

 

4027051

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Dan Abdul Basit ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha