Da yake zantawa da Al-Alam, shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas bayan ganawarsa da Amir Abdullahian ya ce: A yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Iran, an yi nazari kan abubuwan da suke faruwa a Falasdinu, inda suka tattauna da shi kan gudunmawar da a Iran take bayarwa, wajen tallafawa al'ummar Palastinu.
Ya kara da cewa: Mun sanar da ministan harkokin wajen kasar Iran jin dadinmu matuka kan yadda ake samun kyautatuwar alaka tsakanin Iran da kasashen larabawa.
Ya ce; "Mu a Hamas muna maraba da duk wani hali na nazarin halin da ake ciki a yankin da kuma takaita tasirin Isra'ila," in ji Haniyeh.
Shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas, yayin da yake ishara da gwagwarmayar da Falasdinawa fursunoni suke yi na ‘yantar da kansu daga tsare su bisa zalunci da Isra’ila ke yi a gidajen kurkuku, ya ce: suna goyon bayan hakan, tare da yin kira ga dukkanin bangarori na kasa da kasa das u sauke nauyin da ya rataya kansu na tallafawa wadannan falastinawa.
Ya ce yanzu Nasser Abu Hamid, wani fursuna Palasdinawa da ke hannun gwamnatin sahyoniyawan yana cikin mawuyacin hali na rashin lafiya, tare da nuna halin ko in kula da rayuwarsa da Isra’ila ke yi.