Tashar Russia Taoday ta bayar da rahoton cewa, karar fashewar bama-baman ta girgiza babban birnin kasar ta Somaliya a yau da rana tsaka, inda jama’a da dama suka kidime..
An dai kai harin ne a kusa da filin jirgin saman Mogadishu, a cewar majiyoyin gwamatin kasar.
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane takwas tare da jikkata wasu da dama.
Kungiyar ta'addanci ta al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin kamar yadda ta saba yi, inda ta yi ikirarin cewa ta kai harin ne a kan wani ayarin motocin da ke dauke da wasu jami'ai farar fata.
Mohammad Abdi, jami'in tsaro a birnin Mogadishu, ya ce an samu barna a wurin da fashewar ta faru, yana mai nuni da yiwuwar karuwar asarar rayuka.
Kungiyar Al-Shabaab da ke ikirarin kusanci da al-Qaeda, tana fafatawa da gwamnatin tsakiyar Somaliya tun shekara ta 2008, inda daga lokaci zuwa lokaci kungiyar ta kai munanan hare-hare a Mogadishu da wasu sassan kasar, tare da kashe mutane masu tarin yawa.