IQNA

Kotun Kolin Indiya Za Ta Binciki Masu Addinin Hindu Da Ke Nuna Kyama Ga Musulmi

19:53 - January 15, 2022
Lambar Labari: 3486821
Tehran (IQNA) Kotun kolin Indiya ta sanar da cewa za ta yi nazari kan tuhumar da ake yi wa wasu jagororin addinin Hindu masu tsatsauran ra'ayi saboda yin jawabai masu tayar da hankali a kan musulmi yayin wani zaman da ake yi na sirri.

Alkalai uku ne kotun koli suka ce suna yin gargadi ga gwamnatin jihar Utarakand, inda suka bukaci kotun kolin da ta duba batun a mako mai zuwa.

A wani taron da suka yi a watan jiya shugabannin addinan masu tsattsauran ra'ayi sun yi kira ga mabiya addinin Hindu da su yi amfani da makamai domin kisan gillar a kan musulmi.

‘Yan sanda sun ce suna yi wa wadanda ake zargin tambayoyi, amma ba a tsare su ba.

Jihar Uttar Pradesh dai na karkashin jam'iyyar Bharatiya Janata Nationalist Party ne, da ke karkashin jagorancin Firayim Minista Narendra Modi, wanda hawansa mulki a shekara ta 2014 da sake zabensa a shekara ta 2019 ya haifar da karuwar hare-hare kan musulmi da sauran tsiraru a kasar India.

A watan da ya gabata, 'yan sandan Indiya sun kama wani shugaban addinin Hindu mai suna Kalicharan Maharaj, da laifin zagin shugaban 'yancin kai na Indiya Mahatma Gandhi da kuma yabon wanda ya kashe shi.

Wani dan Hindu mai tsatsauran ra'ayi ya harbe Mahatma Gandhi yayin wani taron addu'a a babban birnin Indiya a shekara ta 1948, saboda kokarin da yake yi na ganin ya kawo karshen kyamar musulmi da kuma hada kan alummar India baki daya.

Mahatma Gandhi Jagoran siyasa ne na Indiyawa da ya jagoranci al'ummar Indiya wajen samun 'yanci daga mulkin mallaka na Burtaniya.

 

4028116

 

 

captcha