IQNA

Falastinu Ta Bukaci A Kafa Kwamitin Binciken Ayyukan Laifin Yaki Na Isra'ila

17:36 - January 23, 2022
Lambar Labari: 3486855
Tehran (IQNA) Ma'aikatar harkokin wajen Falasdinu a jiya Asabar ta yi kira da a kafa wani kwamitin kasa da kasa da zai binciki zaluncin da Isra'ila ta yi a shekara ta 1948.

Bayanin hakan ya zo ne bayan da jaridar Haaretz ta Hebrew ta bayyana gano wani kabari na shahidan Palasdinawa na kauyen Tantoura (a arewacin Falasdinu), wanda ‘yan daba ‘yan sahayoniya suka yi wa kisan kiyashi a shekarar 1948.

Sanarwar ta ce: Laifukan 'yan mamaya bai tsaya a shekara ta 1948 ba, don haka ya zama dole a fara bincike kan wadannan laifuka tare da kafa wani kwamitin bincike mai zaman kansa na kasa da kasa da zai binciki su.

Haka kuma kwamitin ne za a dorawa alhakin yin nazari a kan dukkan shari’o’in, sauraron shaidu da tilastawa ‘yan mamaya bude rumbun adana bayanai domin fayyace gaskiya da kuma girman laifukan da aka aikata.

A cewar jaridar, kimanin Falasdinawa 200 ne aka binne a wani babban kabari bayan kashe su, wanda a yanzu ke karkashin wani wurin ajiye motoci a bakin teku.

A baya dai masana tarihi na Falasdinu sun bayar da rahoton kisan gillar da aka yi wa falastinawan yankin Tantura a daren 22 da 23 ga Mayu, 1948.

A cewar masana tarihi, kungiyoyin Yahudawa masu dauke da makamai sun aiwatar da kisan kiyashi da dama a kauyukan Falasdinawa a lokacin yakin 1948, wanda ya tilastawa mazauna garin gudu.

 

4030496

 

captcha