IQNA

Iran Ta Kai Taimako Ga Wadanda Suka Samu Raunuka A Herat Afghanistan

22:59 - January 23, 2022
Lambar Labari: 3486858
Tehran (IQNA) Yayin da adadin mutanen da suka mutu da kuma jikkata sakamakon harin da aka kai a daren jiya a birnin Herat na kasar Afganistan ya kai 16, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta dauki wadanda suka jikkata zuwa kasarta domin yi musu magani.

Jakadan kasar Iran a Herat ya jajantawa iyalan wadanda harin ta'addancin ya rutsa da su a daren ranar Asabar 22 ga watan Janairu inda ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta dauki  wadanda suka samu munanan raunuka sakamakon wannan harin ta'addanci domin yi musu magani.

Babban jami'in jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Herat a wata wasika da ya aike wa "Yaghoub Ali Nazari" gwamnan Khorasan Razavi ya shirya mika wadanda suka jikkata zuwa kasar Iran domin yi musu magani.

Wasikar ta bayyana cewa, da dama daga cikin wadanda harin ta'addancin na daren jiya ya rutsa da su na cikin mawuyacin hali, kuma suna bukatar kulawa cikin gaggawa a wata cibiya ta musamman a Iran.

 

4030585

 

 

 

captcha