IQNA

Hamas Ta Bayyana Ganawar Jami'an Gwamnatin Falastinu Da Isra'ila A Matsayin Cin Amana

21:24 - January 24, 2022
Lambar Labari: 3486861
Tehran (IQNA) Hamas ta bayyanawar da ta gudana tsakanin jami'an gwamnatin Falastinu da Isra'ila a matsayin cin amanar al'ummar falastinu.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa,a  cikin bayanin da hamas ta fitar kan ganawar ministocin gwamnatin falastinu da na Isra'ila, ta bayyana cewa, bai kamata gwamnatin Falastinu ta zama tamkar rakumi da akala ba.

Ministan harkokin wajen Isra’ila, Yair Lapid, ya gana da ministan kula da harkokin fararen hula na Falasdinu Hussein Al-Seikh, wanda ya kasance ganawa irinta ta farko ta M.Lapid da wani jami’in Palasdinu.
Da yake tabbatar da ganawar a shafinsa na tuwita Jami’in na Falasdinu, ya ce sun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi siyasa da kuma alaka ta tsakanin juna.

Hussein al-Sheikh, ya ce sun tattauna hanyoyin samar da wata mafita ta siyasa tsakanin bangarorin biyu bisa tanadin dokokin kasa da kasa, musamman kan rikicin falasdinun da Isra’ila.

Saidai jami’in fayyace ko a ina tattaunawar ta wakana ba.

A nata bangare dai ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila ta ki cewa uffan kan tattaunawar amma bata musanta ganawar ba.

 

4030878

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: martani a matsayin
captcha