IQNA

Kwamishinar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a kara matsin lamba kan Myanmar

21:42 - January 29, 2022
Lambar Labari: 3486881
Tehran (IQNA) Babbar kwamishiniyar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya Michel Bachelet ta yi kira da a kara matsin lamba a duniya kan gwamnatin mulkin sojan Myanmar domin kawo karshen cin zarafin jama'arta.

Tashar  Aljazeera ta habarta cewa, hukumar kare hakkin bil-Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga shugabannin kasashen duniya da su kara matsa lamba ga mahukuntan sojin Myanmar domin kawo karshen cin zarafin jama'ar kasar tare da maido da mulkin farar hula cikin gaggawa.
 
Kusan shekara guda bayan da sojoji suka karbi mulki a kasar, babbar jami'ar kare hakkin bil'adama a MDD Michel Bachelet, ta bayyana cewa al'ummar kasar sun rasa 'yancinsu.
 
Yayin da duniya baki daya ta yi Allah-wadai da juyin mulkin da tashin hankalin da ya biyo baya, in ji Bachelet, ta kira matakin da kasashen duniya suka dauka da cewa ba shi da tasiri, kuma kasashen duniya  ba su da azamar gaggawa da ta yi daidai da girman rikicin.
 
Ofishin kula da harkokin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya OCHA ya bayyana a cikin wani rahoto cewa akalla mutane 1,500 ne sojoji suka kashe a wani yunkurin murkushe masu adawa da juyin mulkin, yayin da wasu dubbai kuma aka jikkata su.
 
Rahoton ya kara da cewa akalla mutane 290 ne suka mutu a gidan yari, mai yiwuwa da yawa daga cikinsu saboda azabtarwa.
 
A cikin watan Maris mai zuwa ne dai ofishin jami'ar ya shirya zai fitar da wani rahoto da ke bayyana halin da ake ciki na hakkin bil'adama a Myanmar tun bayan juyin mulkin da aka yi.
 
 
https://iqna.ir/fa/news/4032157
captcha