IQNA

Saudiyya ta bukaci takardar shedar "halal" ga duk kayayyakin abinci

22:56 - January 30, 2022
Lambar Labari: 3486886
Tehran (IQNA) Babban Daraktan Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Saudi Arabiya ya wajabta bayar da takardar shaidar “halal” na wasu kayayyakin abinci daga farkon watan Yuli mai zuwa.

Wasu kamfanonin abinci a Saudi Arabiya suna buƙatar dokokin fasaha na yankin Gulf tare da sanya alamar halal a kan samfuran abincin da suke shigo da shi a kasar, musamman naman dabbobi.

Wannan doka ta ƙunshi duk wani abinci da aka samar daga gelatin, collagen, cukui na dabba, mai da kitsen dabbobi, ko danye, ko a cikin abincin da ke amfani da nama, kaji da dangoginsu.

A daya hannun kuma, hukumar ta gindaya sharuddan illolin da ke tattare da kayan kwalliya, ga masana’antu masu shigo da kaya da masu sayar da kayan kwalliya, dole ne su dauki matakan da za su iya ba da rahoton illolin da wadannan kayayyakin ke haifarwa ga mutane  a cikin kasar Saudiyya da kuma zama masu kula da kayan bisa ka'ida.

4032358

 

 

 

captcha