IQNA

Alhuti Ya Kirayi Al'ummar Yemen Da Su Hada Kansu Domin Fuskantar Makiyansu Na Gaskiya

14:10 - February 02, 2022
Lambar Labari: 3486896
Tehran (IQNA) Jagoran kungiyar gwagwarmayar Ansarullah ta kasar Yemen ya kira Amurka da gwamnatin Isra'ila "makiya na daya" ga musulmin duniya.

Abdul-Malik al-Houthi ya fada a ranar Talata yayin da yake karbar tawagogin kabilu daga sassan kasar Yemen da yaki ya daidaita, cewa "Amurka da Isra'ila na kokarin cin zarafin al'ummar musulmin duniya."

Ya kara da cewa, "Isra'ila da 'yan amshin shatanta na daukar al'ummar Yemen a matsayin makiyansu."

Al-Houthi dai yana magana ne a kan kasashen Larabawa yankin da suka shiga yarjejeniyar daidaitawa da gwamnatin Isra'ila da Amurka ke marawa baya, kuma tun a wancan lokaci suke kokarin mika kansu ga gwamnatin mamaya ta hanyar daidaita alaka da ita.

4033189

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yarjejeniyar daidaitawa
captcha