IQNA

Taliban Ta Bayar Da Izinin Zuwa Jami'a Ga Dalibai Mata A Kasar Afghanistan

23:37 - February 02, 2022
Lambar Labari: 3486899
Tehran (IQNA) A karon farko tun bayan da kungiyar Taliban ta mulki Afghanistan, an bude kofofin jami'o'in gwamnatin kasar ga dalibai mata.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, jami'an Taliban sun sanar da cewa an bude jami'o'in gwamnati ga 'yan mata a larduna shida na Laghman, Nangarhar, Kandahar, Nimroz, Helmand da Farah a ranar Laraba.

Dangane da shigar da 'yan mata a jami'o'in gwamnatinTaliban wasu dalibai mata kadan ne suka halarci azuzuwan da aka ware ta hanyar raba  jinsi.

Hakkokin mata musamman a fannin ilimi na daya daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankali tsakanin gwamnatin Taliban da kasashen duniya.

Duk da sake bude makarantun firamare a Afganistan, makarantun sakandare da jami'o'in gwamnati a galibin lardunan kasar sun kasance a rufe ga 'yan mata tun bayan da 'yan Taliban suka karbe mulki tare da janye sojojin Amurka a watan Agustan da ya gabata.

 

https://iqna.ir/fa/news/4033359

captcha