IQNA

A Karon Farko Bayan Shekaru 15 Sheikh Ra'ida Salah Ya Shiga Cikin Masallacin Quds

21:59 - February 07, 2022
Lambar Labari: 3486922
Tehran (IQNA) bayan korar Sheikh Ra'id Salah daga birnin Quds shekaru 15 da suka gabata a jiya ya samu damar shiga cikin birnin Quds da kuma masallaci mai alfarma.

Jaridar Daily Sabah ta bayar da rahoton cewa, bayan korar Sheikh Ra'id Salah daga birnin Quds shekaru 15 da suka gabata a jiya ya samu damar shiga cikin birnin Quds da kuma masallaci mai alfarma.

A cewar shaidun gani da ido, sojojin Isra'ila sun tare Sheikh Salah a kusa da Bab al-Asbat kafin kafin su ba shi damar shiga masallacin Al-Aqsa.

Sheikh Raed Salah ya samu shiga masallacin ne a daidai lokacin da ake gudanar da Sallar Magariba a ranar Lahadin da ta gabata, kuma kamar yadda shaidu suka tabbatar, ya samu tarba daga dimbin Falasdinawa masu ibada.

Sheikh Raed Salah na daya daga cikin jagororin gwagwarmayar Palasdinawa kuma jagoran Harkar Musulunci ta Falasdinu.

An hana shi shiga Masallacin Al-Aqsa a watan Fabrairun 2007, kuma ya kasance a tsare na tsawon kusan shekaru biyu a kurkukun Isra’ila ba tare da shari’a ba har zuwa 16 ga Agusta 2020.

An sake shi daga gidan yari a ranar 13 ga Disamba, 2021, kuma gwamnatin Sahayoniya ba ta fitar da wata sabuwar dokar hana shiga birnin ba.

 

4034437

 

 

captcha